Najeriya-Boko Haram

Rahoton musamman kan janyewar MDD daga Borno

Abubakar Shekau, shugaban mayakan Boko Haram
Abubakar Shekau, shugaban mayakan Boko Haram AP - TEL

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da dakatar da ayyukanta a wasu sassan arewacin jihar Borno  da ke Najeriya saboda barazanar tsaro da ake fuskanta bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a ofishinta da wasu cibiyoyin kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan jin kai a Damasak da ke  arewacin jihar. 

Talla

A wata sanarwa dauke da sa hannun babban jami’nta mai kula da harkokin jin kai na Najeriya Mr. Edwar Kallon, majalisar ta ce, harin da mayakan Boko Haram suka kaddamar tare da kona ofishinta da na wasu kungiyoyin jin-kai, aikin ta’addanci ne.

A cewarta, masu aikin jin-kai ba su da laifi da za su cancanci irin wannan hari abun da ke nuna irin barazanar da ma’aikatan jin-kai ke fusknata a wannan yankin.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Bilyaminu Yusuf daga birnin Maiduguri

Rahoton kan dakatar da ayyukan MDD a Borno

Majalisar Dinkin Duniyar ta nuna danuwa kan halin da dubban ‘yan gudun hijira za su shiga a sanadiyyar wannan mataki inda suka nemi hukumomi su yi abun da ya dace don magance matsalolin tsaron saboda a samu damar isa ga ‘yan gudun hijira don taimaka musu.

‘Yan gudun hijira sun koka da wannan yanayi da suka ce za su sake fadawa cikin mawuaycin hali bisa wadanda su ke ciki a halin yanzu.

Daya daga cikin 'yan gudun hijirar ya shaida wa RFI hausa cewa, "Yanzu mutanen NGO da suke kai mana taimako sun ce ba za su iya zuwa ba, bamu san halin da muke ciki ba, ya kamata gwamnati ta kawo mana dauki ga mata ga yara ga azumi ya zo kuma ga wahala".

Yawancin masu aikin jin kai da suka tsere daga yankunan sun bayyana cewa dole ce ta sa su barin wuraren ayyukansu.

Daya daga cikin ma'aikatan jin-kan a yankin Damasak ya ce, "Mu ma'aikatan jin-kai muna fuskantar barazanar tsaro,  kusan kullum in za a kawo hari yana shafar mu domin yawancin ma'aikatanmu ma suna barin aikin saboda barazanar da muke fuskanta, idan ba magance barazanar tsaron ba dubun mutane za su shiga mawuyacin hali".

Yanzu haka ana bayyana damuwa kan halin da ‘yan gudun hijirar suka samu kansu a ciki musamman ganin yadda suke fama da karancin abinci.

Ya zuwa yanzu hukumomi sun ki cewa komai kan wannan hali da ayyukan jin-kai suka samu kansu a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.