Najeriya - Tsaro

Najeriya: Gwamnonin kudu maso gabas sun kafa sabuwar rundunar tsaro

Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya. © @Hope_Uzodimma1/Premium Times

Batun tsaro na cigaba da zama babban abin da ake tafka muhawara kai a Tarayyar Najeriya duk da kokarin hukumomin kasar na murkushe matsalar tsaron, ganin yadda ‘yan bindiga masu satar jama’a domin kudin fansa ke da yiwa jama’a barazana a arewacin kasar, yayin da kuma a yankin kudanci aka fuskanci hare-haren ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne.

Talla

A jihar Imo dake yankin kudu maso gabashin Najeriya, cikin makon jiya ‘yan bindiga suka sake kaddamar da farmaki kan hedikwatar ‘yan sanda da ke karamar Hukumar Mbaitoli da safiyar ranar Alhamis tare da sace wani jami’in tsaro, ko da yake daga bisani rahotanni sun ce an sako jami’in.

Harin ya zo ne kwanaki uku bayan da ‘yan bindigar suka kai makamancin wannan farmakin kan shalkwatan ‘yan sandan da kuma Gidan Yarin Gyara Halinka na garin Owerri tare da kubutar da fursunoni  dubu 1 da 884.

Wasu jami'an tsaron Najeriya a birnin Fatakwal.
Wasu jami'an tsaron Najeriya a birnin Fatakwal. AP - SCHALK VAN ZUYDAM

A kokarinsu na kawo karshen matsalar tsaron da ke karuwa, Gwamnonin yankin kudu maso gabashin Najeriya a karkashin jagorancin gwamnan Ebonyi Dave Umahi a jihar Imo, sun sanar da kafa rundunar tsaron da suka sanyawa suna EBUBE AGU wadda suka dorawa alhakin murkushe barazanar jama’ar yankin ke fuskanta daga masu aikata muggan laifuka.

Kafa sabuwar rundunar tsaron da gwamnonin suka yi dai ya haifar da muhawara kan matakin, inda wasu ke yabawa da matakin bisa cewar sun yi daidai, a yayin da wasu ke kallon hakan a matsayin alamar dake kara nuna gazawa daga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Yayin tsokaci kan halin da ake ciki a lokacin tattaunawa da Garba Aliyu Zaria Dakta Hakeem Baba-Ahmed kakakin kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ya bayyana kafuwar sabbin rundunonin tsaron yankuna cigaban mai hakon rijiya ne, domin kamata yayi gwamnati ta sauke nauyin da yake kanta na inganta tsaro ta hanyar kara yawan jami’an tsaron da kuma basu kayan aiki.

Dakta Hakeem Baba Ahmed kan matakin Gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya na kafa rundunar tsaron yankin
Dakta Hakeem Baba Ahmed kan matakin Gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya na kafa rundunar tsaron yankin

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.