Najeriya - Siyasa

Kuri’un jama’a suka cancanci raba gardamar zabe ba kotuna ba – Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bayan isa kasar Mali a matsayin mai shiga tsakanin sasanta rikicin siyasar kasar.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bayan isa kasar Mali a matsayin mai shiga tsakanin sasanta rikicin siyasar kasar. AP - Baba Ahmed

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bukaci gudanar da sauyi ga tsarin zabuka a kasar domin kawo karshen tasirin yin amfani da kudade wajen murde sakamakon zabuka.

Talla

Yayin zantawa da manema labarai a birnin Abuja, Jonathan ya ce kamata yayi kuri’un jama’a su rika tantance ‘yan takarar da suka yi nasara a zabe ba sai an kai ga kotuna ba, ko da yake a cewar tsohon shugaban danganawa da kotunan shi ma tsarin dimokaradiya ne.

Sai dai Jonathan ya ce muddin ya zamana kotuna ne ne ke raba gardamar sakamakon zabuka a mafi akasarin lokuta, ba wai kuri’un jama’a ba, to fa babu shakkah da sauran rina a kaba dangane da kokarin Najeriya na zama kasa mai baiwa tsarin mulkin dimokaradiya cikakken hakkin da ya kamata.

Wata mata yayin kada kuri'ar yayin zaben shugaban kasa a birnin Lagos dake Kudancin Najeriya. 14/04/2007.
Wata mata yayin kada kuri'ar yayin zaben shugaban kasa a birnin Lagos dake Kudancin Najeriya. 14/04/2007. AP - SUNDAY ALAMBA

Tsohon shugaban Najeriyar ya bada misali da Tanzania inda ya ce laifi ne babba a kasar idan aka samu dan takara ya buga sunansa ko kuma hotonsa akan wata kyauta domin baiwa jama’a domin neman kuri’arsu, salon da dade da samun gindin zama a Tarayyar Najeriya.

Sai dai masu sharhi kan lamurran yau da kullum a ciki da wajen Najeriya na ganin cimma wannan buri dai abin da kamar wuya ‘wai gurguwa da auren nesa, domin wannan ba shi karo na farko da ake yin makamancin wannan yunkuri na kyautata tsarin zaben kasar ba, a cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge na tsangayar nazarin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero dake Kano.

Farfesa Kamilu Sani ya kara da cewar yunkurin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ba zai yi tasiri ba, la’akari da cewar ba shi da mukamin da zai iya kawo wannan gayara kamar yadda ya bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.