Najeriya-Polio

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yiwuwar sake samun Polio a Najeriya

Shekara ta 2 kenan ba a samu bullar cutar ta Polio a sassan Najeriya yayinda WHO ta wanke kasar daga jerin masu fama da cutar.
Shekara ta 2 kenan ba a samu bullar cutar ta Polio a sassan Najeriya yayinda WHO ta wanke kasar daga jerin masu fama da cutar. AFP/File

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar akwai yiwuwar sake samun cutar polio mai zafi a Najeriya muddin aka gaza wajen daukar matakan kariya.

Talla

Elizabeth Onitolo, jami’ar hukumar UNICEF ta bayyana haka lokacin da ta ke gabatar da mukala kan abinda zai biyo bayan nasarar da aka samu wajen dakile cutar bayan da aka wanke Najeriya daga samun ta.

Onitolo ta ce har yanzu nasarar da Najeriya ta samu na wanke ta daga kasashen da suka yi fama da cutar ta polio na rawa saboda yadda aka samu koma baya wajen ci gaba da gabatar da allurar rigakafin ta, abinda ya sa yara da dama suka kasa samun allurar.

Jami’ar ta ce bayan karancin bada allurar ana kuma fuskantar matsalolin tsaftar muhalli da kula da lafiya a cikin al’ummomi daban daban wadanda ke iya bada damar samun barkewar cutar.

Onitolo ta ce hanya guda da za a dakile samun cutar ita ce ta gabatar da allurar rigakafin ga kowanne yaro da kuma tabbatar da samun garkuwar kariya a jikin yara.

Jami’ar ta ce babu dalilin da yara za su dinga mutuwa dalilin gamuwa da cutar da ake iya samar mata da maganin kariya, musamman ganin yadda aka kwashe shekaru 2 a Najeriya ba tare da samun cutar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.