Najeriya - Borno

Mayakan Boko Haram sun kai sabon farmaki kan garin Damasak

Shugaban mayakan Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban mayakan Boko Haram Abubakar Shekau REUTERS - HANDOUT

Rahotanni daga Najeriya sun ce mayakan boko haram sun kaddamar da sabbin hare hare a garin Damasak yau talata, kwanaki bayan kona sansanin yan gudun hijira a garin.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace maharan akan motocin dake dauke da makamai sun kai harin ne yau da misalin karfe 5 na yamma, wanda ya shafi cibiyar soji da kuma matsugunin su, abinda ya haifar da musayar wuta.

Garin Damasak dake kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar ya dade yana fuskantar hare haren mayakan boko haram.

Ko a ranar asabar sanda mayakan book haram suka kai hari garin inda suka kona matsugunin kungiyoyin agaji ciki harda na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke dauke da kungiyoyi da dama.

Akalla mutane 4 suka mutu a harin ciki harda soja guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.