Najeriya - Faransa

Ministan harkokin wajen Faransa kan kasuwanci na ziyara a Najeriya

Franck Reister, Ministan Turai da harkokin wajen Faransa dake kula da kasuwancin kasashen ketare.
Franck Reister, Ministan Turai da harkokin wajen Faransa dake kula da kasuwancin kasashen ketare. AP - Michel Euler

Yanzu haka tawagar ministan Turai da harkokin wajen Faransa dake kula da kasuwancin kasashen ketare Franck Reister na ziyarar kwanaki biyu a Najeriya, inda ake sa ran a yau za ta gana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ministan kasuwanci Niyi Adebayo da na kudi Zainab Ahmed a birnin Abuja.

Talla

Ana sa ran bangarorin biyu sun tattauna harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu ta yadda kowanne bangare zai samu cigaba.

Tawagar ta kasar Faransa za ta kuma isa birnin Lagos gobe Laraba inda za ta gana da yan kasuwa cikin su harda fitaccen attajirin kasar Abdusamad Isykau Rabiu mai kamfanin BUA.

Idan dai ba a manta ba AbduSamad na hadin gwuiwa da kasar Faransa wajen gina katafaren matatar mai a Jihar Cross Rivers dake Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.