Najeriya-Boko Haram
Addu'o'i sun mamaye taron cika shekaru 7 da sace daliban Chibok
Wallafawa ranar:
Yau aka cika shekaru 7 da sace daliban sakandaren Chibok mata sama da 250 da mayakan boko haram suka yi, kuma har ya zuwa wannan lokaci ba a ga wasu daga cikin su ba.Sakamakon wannan al’amari yau an gudanar da addu’oin addinin Musulunci da na Kirista domin ganin an sako wadanda suka rage. Daga Maiduguri ga rahoton Wakilinmu Bilyaminu Yusuf.