Najeriya - Lafiya

Duk mutum 1 daga cikin 'yan Najeriya 4 na fama da tabin hankali - Bincike

'Yan Najeriya yayin hada hada a wani yanki na birnin Legas.
'Yan Najeriya yayin hada hada a wani yanki na birnin Legas. ASSOCIATED PRESS - Lekan Oyekanmi

Wani masanin harkar kula da lafiya dake Jami’ar Ilorin a Najeriya, Farfesa Bamidele Owoyele ya bayyana cewar cikin kowanne Yan Najeriya guda 4 da aka gani, guda daga cikin su na fama da matsalar tabin hankali, abinda ke nuna cewar kashi guda bisa 4 na mutanen kasar miliyan 200 na fama da wannan matsala.

Talla

Yayin da yake gabatar da mukala a taron masanan kula da lafiya ta duniya wanda aka shirya tare da Cibiyar Binciken kwakwalwa a Jami’ar Ilorin, Farfesan yace yawan mutanen dake fama da matsalar tabin hankali ko kuma cutar dake da nasaba da kwakwalwa na karuwa a cikin kasar.

Shehun malamin ya danganta wannan matsalar da shan sinadarin dake dauke hankali ko kuma magungunan da suka sabawa umurnin likita.

Yankin Oshodi dake jihar Legas a tarayyar Najeriya.
Yankin Oshodi dake jihar Legas a tarayyar Najeriya. ASSOCIATED PRESS - GEORGE OSODI

Farfesa Owoyele ya bukaci gwamnatoci a kowanne matakai da su kara yawan kasafin kudin da suke warewa harkar kula da lafiyar jama’a a koda yaushe, inda yake cewa kashi 2 na kudin da ake warewa yanzu haka yayi kadan.

Masanin ya kuma bukaci masu hannu da shuni a Najeriya da su bi sahun takwarorin su na kasashen duniya wajen bada gudumawar kudaden da za’a gudanar da bincike domin samo hanyar magance cututtukan da suka shafi kwakwalwa.

Shehun malamin ya kuma bukaci sake horar da masana da jami’an kula da harkar lafiya domin cike gibin da ake da shi na masu kula da lafiyar jama’a ganin yawan mutanen da ake da shi a Najeriya da kuma samo hanyar rage yawan likitocin dake barin kasar zuwa kasashen duniya domin yin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.