Najeriya - Faransa

Faransa ta karfafa zawarcin 'yan kasuwar Najeriya

Ministan kula da kasuwancin kasashen ketare na kasar Faransa Franck Riester tare da shugaban kamfanin BUA Alhaji AbduSamad Isayaka Rabi'u.
Ministan kula da kasuwancin kasashen ketare na kasar Faransa Franck Riester tare da shugaban kamfanin BUA Alhaji AbduSamad Isayaka Rabi'u. © RFI Hausa/Ahmed Abba

Karamin Minista mai kula kasuwancin kasashen waje na Faransa, Franck Riester, ya ƙarƙare ziyarar kwanaki biyu da ya kaai Najeriya a ranar Laraba, da zummar karfafa alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu da kuma mika goron gayyata ga mahalarta manyan taruka biyu na tattalin arzikin Afrika da Faransa, da shugaba Emmanuel Macron zai dauki nauyi a watannin Mayu da Yuli mai zuwa.

Talla
Ministan kula da kasuwancin kasashen ketare na kasar Faransa Franck Riester tare da hamshakin attajirin Nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote.
Ministan kula da kasuwancin kasashen ketare na kasar Faransa Franck Riester tare da hamshakin attajirin Nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote. © RFI Hausa/Ahmed Abba
Bayan ganawa da da mataimakin shugaban Najeriya Abuja, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Kungiyar gwamnonin Najeriya, ministan harkokin kasuwancin wajen na Faransa Frank Riester ya isa Legas ranar Laraba, inda ya gana da manyan shugabannin kungiyar zuba jari ta Faransa da Najeriya da Emmanuel Macron ya kaddamar a watan Yulin shekarar 2019 lokacin da ya kawo ziyara Najeriya.

Ahmed Abba ya hada rahoto kan ziyarar tawagar gwamnatin Faransar a tarayyar Najeriya.

Rahoto kan ziyarar wakilan gwamnatin Faransa a Najeriya domin zawarcin 'yan kasuwar kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.