Najeriya - Kano

Ganduje ya sasanta Dangote da BUA

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da Hamshakin dan kasuwa Alhaji Alhassan Dantata, bayan sasanta hamshakan attajirai Alhaji Aliko Dangote da AbduSamad Isyaka Rabi'u.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da Hamshakin dan kasuwa Alhaji Alhassan Dantata, bayan sasanta hamshakan attajirai Alhaji Aliko Dangote da AbduSamad Isyaka Rabi'u. © tribuneonlineng.com

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sansanta Alhaji Aliko Dangote da kuma AbduSamad Isyaka Rabi’u hamshakan attajirai a nahiyar Afrika guda biyu ‘yan asalin jihar ta Kano.

Talla

Bayanai sun ce gwamnan Kanon ya jagoranci taron sulhun ne a birnin Abuja yau Alhamis.

A ‘yan kwanakin nan dai rahotanni sun bayyana yadda dangantaka tayi tsami tsakanin attajiran biyu, dangane da batun daidaita farashin sukari da kamfanoninsu ke samarwa a cikin Najeriya.

Wadanda suka halarci taron sasancin sun hada da Ministan kasuwanci Najeriya da bunkasa zuba hannayen jari Niyi Adebayo, wakilin masarautar jihar Kano Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, da shugaban majalisar malaman Kano Shiekh Muhammad Nasir Adam limamin babban Masallacin Tijjaniya na kofar Mata a Kano, da kuma Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.