Najeriya - Tattalin Arziki

Hauhawar farashin kayayyaki ya zarce kashi 18 a Najeriya

Wata kasuwar saida kayayyakin abinci a birnin Legas dake kudancin Najeriya.
Wata kasuwar saida kayayyakin abinci a birnin Legas dake kudancin Najeriya. AP - Sunday Alamba

Hukumar kula da kididdiga a Najeriya ta sanar da samun hauhawar farashin kayayyaki a watan Maris wanda ya kai kashi 18.17 sakamakon tashin farashin kayan abinci da aka gani.

Talla

Wannan sabon adadin ya zarce wanda aka gani a watan Fabarairu wanda ya kai kashi 17.33, kuma daga cikin alkaluman da hukumar ta gabatar ya nuna cewar an samu karin farashin abinci da ya kai kashi 22.95 sabanin wanda aka gani a watan Fabarairu na 21.79.

Wata mai sayar da kayan gwari a kasuwar unguwar Obalande dake birnin Legas.
Wata mai sayar da kayan gwari a kasuwar unguwar Obalande dake birnin Legas. AP - Sunday Alamba

Masana tattalin arziki na danganta hauhawar farashin da tsadar rayuwa da kuma matsalolin da Najeriya ke fuskanta na rashin tsaro dake hana manoma zuwa gonakin su.

Alkaluman hukumar sun ce an fi samun hauhawan farashin a Jihohin Rivers da Niger da kuma Gombe, yayin da aka samu akasin haka a Jihohin Zamfara da Yobe da kuma Kebbi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.