Najeriya-Boko Haram

Najeriya: Mutane fiye da dubu 100 sun tsere daga Damasak zuwa Nijar

Wani yanki dake wajen garin Damasak dake jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wani yanki dake wajen garin Damasak dake jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya. AP - Jerome Delay

Rahotanni daga Najeriya sun ce mutane sama da 100,000 ne suka tsere zuwa Jamhuriyar Nijar daga garin Damasak dake jihar Borno, bayan kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai garin har sau biyu a cikin mako guda.

Talla

Majiyoyi da dama sun tabbatar da hasarar rayukan da aka yi a hare haren, da kuma dimbin dukiyar da aka rasa.

Wani mazaunin garin Bulama Ahmadu ya shaidawa RFI Hausa cewar yanzu haka rabin mazauna garin na Damasak sun tsere domin tsira da rayukan su duk da kokarin da sojoji ke yi na hana su tafiyar.

Wani Dattijo mazaunin garin Damasak dake jihar Borno a Najeriya.
Wani Dattijo mazaunin garin Damasak dake jihar Borno a Najeriya. AP - Jerome Delay

Ahmadu yace ganin yadda garin ke da karancin jami’an tsaro da kuma yadda 'yan bindigar suka dinga kai farmaki a cikinsa, barin garin shi ne mafi alheri a garesu domin samun mafaka inda za su tsira da rayukansu.

Garin Damasak na da nisan kilomita 188 daga birnin Maiduguri dake Jihar Barno, kuma yana da matukar tasiri ga harkokin kasuwanci saboda kasancewar sa kusa da iyakokin Jamhuriyar Nijar da Tafkin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.