Najeriya-Kwaya

An kama 'yan Chadi da Nijar masu sayar wa 'yan ta'addan Najeriya kwaya

Wasu jami'an NDLEA a Najeriya
Wasu jami'an NDLEA a Najeriya NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wasu mutanen Chadi da Nijar da ke safarar kwayoyi ga ‘yan ta’adda a Najeriya.

Talla

NDLEA ta cafke mutanen ne a makon da ya gabata a jihohin Taraba da Niger kamar yadda shugabanta, Buba Marwa ya bayyana a birnin Abuja a yayin wata ziyara da ya kai wa Ministan Yada Labarai na kasar, Lai Mohammed.

Marwa ya ce, sun kama masu fataucin kwayoyin su dubu 2 da 175, sannan suka kwace haramtattun kwayoyi masu nauyin kiliogram 2,050,765.33.

Kudaden da NDLEA ta karbe da kuma darajar kwayoyin sun kai  Naira biliyan 75 kamar yadda Marwa ya bayyana.

Shugaban na NDLEA ya ce, ‘yan Najeriya miliyan 15 da shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 60, na ta'ammuli da kwayoyi, kuma kashi 25 na wannan adadi mata ne a cewarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.