Najeriya - PDP

Dalilin da ya sa muka yiwa Goodluck Jonathan bore - Babangida

Tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu
Tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu © The Guardian Nigeria

Tsohon Gwamnan Jihar Naija dake Najeriya Babangida Aliyu ya bayyana dalilin da ya sa Gwamnonin Jam’iyyar PDP suka bijirewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a shekarar 2015 lokacin da ya tsaya takarar neman wa’adi na biyu.

Talla

A wata sanarwar da ya rabawa manema labarai, tsohon Gwamnan yace sun dauki matakin ne saboda karyar alkawarin da yayi cewar ba zai tsaya takara ba bayan kamala wa’adin tsohon mai gidan sa Umaru Yar’adua da kuma samaun nasarar zaben shekarar 2011.

Babangida yace daukacin Gwamnonin sun marawa Jonathan baya lokacin da Yar Adua ya rasu da kuma takarar sa ta shekarar 2011, amma hakikancewar sa cewar zai zarce a shekarar 2015 ya gamu da fushin su domin hakan ya saba ka’ida kuma hakkin sa ne a matsayin shugaban gwamnonin arewacin kasar ya fito yayi bayani akai.

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan yayin yakin neman zabe a shekarar 2015.
Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan yayin yakin neman zabe a shekarar 2015. AP - Sunday Alamba

Tsohon Gwamnan yace ba wai sun nunawa Jonathan kiyayya bane, sai dai sun dauki matakin ne domin kare muradun jama’ar yankin dangane da alkawarin da suka yi a rubuce wanda aka sanya hannu akai cewar tsohon shugaban ba zai sake takara ba.

Babangida Aliyu yace abin takaici ne da yau za’a kira sunan sa ana cewa shine yake adawa da takarar Goodluck Jonathan a shekarar 2015.

Yanzu haka dai Jam’iyyar PDP a karamar hukumar Chanchaga ta dakatar da tsohon Gwamnan saboda abinda ta kira zagon kasa da kuma wasu harkoki da suka sabawa Jam’iyar ta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.