Najeriya - Damasak

Rundunar sojin Najeriya ta musanta tserewar dubban mutane daga Damasak

Ibrahim Ousmane, wani mazaunin garin Damasak da ya tserewa farmakin mayakan Boko Haram a cikin watan Nuwamban 2020.
Ibrahim Ousmane, wani mazaunin garin Damasak da ya tserewa farmakin mayakan Boko Haram a cikin watan Nuwamban 2020. RFI/Nicolas Champeaux

Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin dake cewa mutane fiye da dubu 100 sun tsere daga garin Damasak zuwa cikin Jamhuriyar Nijar, sakamakon farmakin mayakan Boko Haram.

Talla

Yayin tabbatar da rahotannin a ranar Alhamis, wani mazaunin garin Bulama Ahmadu ya shaidawa RFI Hausa cewar yanzu haka rabin mazauna garin na Damasak sun tsere domin tsira da rayukan su duk da kokarin da sojoji ke yi na hana su tafiyar.

Sai dai a yayin tashi zantawar da sashin Hausa na RFI, Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya Janar Muhammad Yarima, ya bayyana mamaki da takaici kan yadda rahoton da ya bayyana a matsayin na karya, ya samu karbuwa a wajen jama’a.

Janar Yarima ya ce mayakan Boko Haram ba su ma samu damar shiga garin na Damasak ba.

Tattaunawa da daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya Janar Muhammad Yarima kan halin da garin Damasak ke ciki
Tattaunawa da daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya Janar Muhammad Yarima kan halin da garin Damasak ke ciki

Bayanin daraktan rundunar sojin Najeriyar dai na zuwa ne bayan da Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane dubu 65 suka fice daga garin na Damasak dake Jihar Barno domin tsira da rayukan su bayan hare haren da mayakan Boko Haram suka kai har sau uku cikin mako guda.

Babar Balock, kakakin hukumar kula da yan gudun hijira na Majalisar yace hare haren sun tilastawa akalla kashi 80 na mazauna Damasak barin garin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.