Najeriya - Zamfara

‘Yan Sa-kai sun kashe ‘yan bindiga a kasuwar Zamfara

Wasu 'Yan Sa-kai dake yakar ta'addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu 'Yan Sa-kai dake yakar ta'addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya. © Reuters/Akintunde Akinleye

Rahotanni daga Jihar Zamfara dake Najeriya sun ce yau juma’a wasu 'yan Sa-kai sun kutsa kasuwar Dansadau inda suka kama wasu da ake zargin 'yan bindiga ne kuma nan take suka halaka su.

Talla

Shaidun gani da ido sun ce 'yan Sa-kan wadanda akasarin su suka fito daga garon Ruwan Rofa da kewaye sun mamaye kasuwar ne wajen zakulo mutanen da suke zargi inda suka hallaka su nan take a kasuwar da ake ci yau wadda ta shafi cinikin dabbobi da kayan abinci.

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar sakamakon lamarin mutane sun gudu daga kasuwar zuwa gidajen su, yayin da gawarwakin wadanda aka kashe ke zube a kasuwar.

Mutumin yace 'yan bindigar sun tare hanyar Gusau zuwa Dansadau abinda ya tilasatawa wasu matafiya zirga zirga, a daidai lokacin da direbobin haya ke yajin aiki saboda abinda suka kira fashi da garkuwa da su da ake yawan yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.