Najeriya

Alkaluman mutanen da aka yiwa allurar Covid 19 a Najeriya

Mutane a titin birnin Lagos a Najeriya. Lagos na daya daga cikin biranen da ake samun masu bahaya a fili
Mutane a titin birnin Lagos a Najeriya. Lagos na daya daga cikin biranen da ake samun masu bahaya a fili Reuters / Akintunde Akinleye

A Najeriya bayan kusan makonni uku da soma yiwa jama’a allurar rigakafin cutar Covid 19,alkaluma na bayyana cewa ya zuwa yanzu kam kusan mutane 370.000 ne suka amfana da wannan allurar.

Talla

Hukumar samar da lafiya ta kasa ta fitar da na ta alkaluma  ajiya juma’a cewa an samu yiwa mutane 374.585 wannan allura,inda aka samu wannan nasara a fadin kasar.

Jihar Kogi na daga cikin yankunan da ba a samu isa da wannan allurar ba a cewar hukumar.

Allurar Astrazeneca
Allurar Astrazeneca JOEL SAGET AFP

Daga cikin johohin kasar da suka amfana da wannan allura,Lagas na da yawan mutane  92.000,Jihar Ogun na a mataki na biyu da mutane  36.959 ,Bauchi mutane 31.321,Kaduna 29.426,Jigawa 22.420 sai Kwara da mutane 20.060.

A Jihohin Kebbi da Taraba mutun daya-daya suka amfana da wannan allura,sai Abia mutane 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.