Najeriya

Arewacin Najeriya ne kadai 'Yan kabilar Igbo ke da lumana-Ohanaeze

Wani yankin yan aware 'Yan kabilar Igbo a Najeriya
Wani yankin yan aware 'Yan kabilar Igbo a Najeriya STEFAN HEUNIS / AFP

Babbar kungiyar 'Yan  kabilar Igbo dake Najeriya ta bayyana cewar babu inda 'ya'an ta ke zaman  lumana da kuma gudanar da harakokin su cikin kwanciyar hankali da ya wuce yankin arewacin kasar.

Talla
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari  sanya da kayan kabilar Igbo
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sanya da kayan kabilar Igbo RFIHAUSA
Shugaban kungiyar a jihohi 19 dake arewacin Najeriya Augustine Amaechi ya sheidawa wani taro a Abuja cewar yankin arewacin kasar ya rungumi 'Yan kabilar Igbo fiye da yadda ake zato wajen basu damar gudanar da harakokin su ba tare da tsangwama ba,abinda ya taimaka musu wajen samun cigaba.

Amaechi wanda ya ce akan dan samu matsala nan da can jifa-jifa amma wannan ba wani abinda zai tada hankali bane musamman a kasar da take kokarin cigaba.

Dangane da batun kafa kasar Biafra da wasu 'Yan kabilar Igbo ke fafutuka a kai,Shugaban  kungiyar ya ce matsalar rashin ayyukan yi a yankin ya sa wasu daukar wannan matsayi,inda ya kara da cewa a matsayin su na 'Yan kabilar Igbo na 'Yan kasuwa suna matukar bukatar yankin arewa domin habakar sana'oin su.

Amaechi yace duk da fushin da matasa suke da shi da kuma bukatar ballewa daga Najeriya,su bukatar su itace sake fasalin kasar amma ba raba ta,domin babu hanyar da za'a sarrafa kaya a kauyen ku kuma kayi kasuwa kamar yadda ake yi yanzu a kasuwar Alaba dake lagos.

A nashi jawabi Shugaban kungiyar Ohanaeze na kasa George Obiozor ya bayyana cewar 'Yan kabilar Igbo basa yaki da kowa,sai dai suna bukatar ganin an basu hakkin su na 'Yan kasa,kuma suna bukatar zaman lafiya da hadin kai da kowanne bangare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.