Najeriya - Tattalin Arziki

Dalilin danganta ni da tsatsauran ra’ayi – Isa Ali Pantami

Shirin tattance masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya
Shirin tattance masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya REUTERS/Robert Galbraith/File Photo

Ministan Sadarwar Najeriya Dr Isa Ali Pantami ya zargi wasu bata gari da neman bata masa suna wajen danganta shi da tsatsauran ra’ayi saboda matakan da yake dauka a gwamnatin Najeriya.

Talla

A wata hira ta musamman da yayi da Jaridar Premium Times da ake wallafawa daga Najeriya, ministan yace babu gaskiya a cikin zargin domin kuwa labarin kanzon kurege ne da wasu dake adawa da shirin gwamnati na hada lambar zama dan kasa da layukan wayoyin sadarwa da aka bukata ga kowanne dan kasa da baki dake zama a Najeriya su ke yadawa.

Pantami yace babu tababa cikin wannan matsayi na shi cewar wannan zargin da ake masa nada nasaba da rajistar da gwamnati ta bukaci kowa yayi, ganin cewar tun daga shekarar 2011 a karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan aka dauko shirin amma bai samu nasara ba saboda yadda wasu ke adawa da shi.

Shugaban hukumar fasahar sadarwar zamani ta Najeriya NITDA Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.
Shugaban hukumar fasahar sadarwar zamani ta Najeriya NITDA Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami. iittelecomdgest.com

Ministan yayi karin haske kan shirin rajistar wanda yace ya shafi duk mazauna Najeriya da suka fito daga wasu kasashe domin tattara bayanan kowanne dan kasa da baki kamar yadda doka ta tanada.

Pantami yace kammala wannan aiki zai taimakawa gwamnato sosai wajen rage aikata laifuffuka saboda yadda za’a dinga amfani da irin wadannan bayanai wajen gano masu laifi.

Ministan yace hare hare da yarfen da ake masa ba zasu sashi sake matsayi ko kuma kawar da hankalin sa daga aikin da ya sa a gaba ba.

Idan dai ba’a manta ba wata Jarida a Najeriya ta zargi ministan da tsatsauran ra’ayi inda tace hukumomin Amurka na sanya ido akan sa, amma daga bisani ta nemi gafara cewar kuskure tayi.

Pantami ya sha alwashin neman hakkin sa a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.