Najeriya

Zamu mamaye gidajen 'Yan Majalisun Najeriya - NULGE

Zauran Majalisar Wakilan Najeriya
Zauran Majalisar Wakilan Najeriya © Femi Gbajaiamila - twitter

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya ta yanke hukuncin mamaye gidajen 'Yan Majalisun tarayyar kasar dake goyan bayan kudirin dokar da ake mahawara akan ta da zummar rusa gwamnatin kananan hukumomin da ake da su a fadin kasar.

Talla

Kungiyar ta bayyana 'Yan majalisun dake goyan bayan kudirin dokar a matsayin makiya Najeriya da dimokiradiyar ta kuma sune basu san muhimmancin samun gwamnati a yankunan karkara ba.

Shugaban kungiyar ta kasa Ambali Olatunji ya bayyana wannan matsayi saboda kudirin dokar da dan majalisar wakilai daga jihar Rivers Bob Solomon dan jam’iyyar PDP ya gabatar.

Olatunji yace muddin ba’a kashe wannan yunkuri da wuri ba, ma’aikatan kananan hukumomin zasu kaddamar da shirin su na zanga zanga zuwa Majalisar dokoki ta kasa da kuma gidajen 'Yan majalisun.

Shugaban kungiyar yace ana barazana da wanzuwar su a matsayin kananan hukumomi, saboda haka ba zasu rungume hannayen su suna kallon ruwan da zai zo ya tafi da su ba.

Anci moriyar ganga

Olatunji yace wadannan 'Yan majalisu da suka ci moriyar kananan hukumomi basa wakilatar su, kuma babu wani dake goyan bayan talakan Najeriya da zai goyi bayan shirin.

A karshen shugaban ma’aikatan ya bukaci gwamnonin da suka amince da wanzuwar kananan hukumomin, suka kuma gudanar da zabuka da su bayyana rashin goyan bayan su ga wannan yunkuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.