Najeriya-Boko Haram

Pantami ya yi watsi da kalamansa na shekarun baya

hanyoyin sadarwa da aka fi amfani da su a Najeriya
hanyoyin sadarwa da aka fi amfani da su a Najeriya ISSOUF SANOGO AFP/File

Ministan Sadarwar Najeria Dr Isa Ali Pantami yayi watsi da wasu kalamai da yayi a shekarun baya da suka shafi kungiyae Al Qaeda da Taliban wadanda suka haifar da cece kuce a yan kwanakin nan.

Talla

Ministan wanda ke fuskantar kiraye kiraye na ya sauka daga mukamin sa saboda wadannan kalamai, ya danganta su da ayyukan abokan gaba wadanda ke adawa da shirin da yake aiwatarwa a cikin gwamnati.

Ministan yace lokacin da yayi wadancan kalamai yana da karancin shekaru ne kuma a cikin jami’a, saboda ya dauki wasu matsayi da a yanzu suka canja.

Shugaban hukumar fasahar sadarwar zamani ta Najeriya NITDA Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.
Shugaban hukumar fasahar sadarwar zamani ta Najeriya NITDA Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami. iittelecomdgest.com

Pantami yace ya kwashe shekaru 15 yana fadakar da jama’a akan illar ta’addanci a Jihohi irin su Katsina da Gombe da Borno da Kano da kuma Diffa dake Jamhuriyar Nijar.

Ministan yace yayi arangama da masu tsatsauran ra’ayin boko haram, kuma ya wallafa kasidu a harshen Hausa da Larabci da kuma Turanci domin janyo hankalin wasu daga cikin masu irin wannan akida, kuma yayi nasarar ceto matasa da dama da suka dauki irin wancan ra’ayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.