Najeriya - Boko Haram

ISWAP ta kashe sojojin Najeriya biyar wasu da dama sun bace a Barno

Makamin roka makale jikin wata mota da mayakan Boko Haram ke amfani da shi a garin Damasak dake jihar Barno, an dauki hoton ranar 18 ga watan Maris shekarar 2015
Makamin roka makale jikin wata mota da mayakan Boko Haram ke amfani da shi a garin Damasak dake jihar Barno, an dauki hoton ranar 18 ga watan Maris shekarar 2015 ASSOCIATED PRESS - Jerome Delay

Sojojin Najeriya biyar sun mutu, hudu kuma sun jikkata sannan da dama sun bace, sakamakon hari da mayakan Boko Haram bangaren ISWAP suka kai wani sansanin su dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Talla

Wasu jami’an soji biyu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewar, Mayakan Boko Haram dake biyeyya ga kungiyar IS, sun fatattaki sojoji daga wani sansani da ke kauyen Kamuya, mai nisan kilomita 35 garin Biu ranar Jumma’a bayan musayar wuta.

"Yan ta'addan sun kashe sojoji biyar tare da jikkata wasu hudu a harin da suka kai sansanin Kamuya," in ji wani jami'in soja da ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Jami'in soji na biyu ya ce "Ya zuwa yanzu sojoji 41 sun dawo yayin da 58 suka bata, kuma ya zuwa yanzu rundunar sojin Najeriya bata ce uffan ba kan wannan rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.