Najeriya

Mutane 12 suka rasa rayukan su sakamakon gobara a Benue

Wasu tankunan Mai da suka kama da wuta
Wasu tankunan Mai da suka kama da wuta REUTERS/Athar Hussain

Rahotanni daga Jihar Benue dake Najeriya sun ce mutane 12 suka rasa rayukan su sakamakon wata gobarar da ta tashi sakamakon fashewar tankin mai a karamar hukumar Agatu.

Talla

Bayanan dake zuwa daga yankin sun ce tankar man ta fadi ne akan hanyar Oshigbudu zuwa Obagaji, inda man dake cikin ta ya kwarara kafin kamawa da wuta.

Hoton bidiyo dake nuna yadda bakin hayaki ya turnuke
Hoton bidiyo dake nuna yadda bakin hayaki ya turnuke AP

Kwamandan hukumar yaki da hadura a Jihar Yakubu Muhammed yace motar ta kwace ne daga matukin ta abinda yayi sanadiyar hadarin.

Jami’in yace daga cikin wadanda suka mutu akwai maza 8 da mata 3 tare da jariri guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.