Najeriya-Arewa

Sai mun ilmantar da talakawa kafin mu samu zaman lafiya-Shettima

Kashim Shettima
Kashim Shettima via thisday

Tsohon gwamnan Jihar Borno da ke Najeriya Kashim Shettima ya koka kan yadda hukumomi da masu hannu da shuni ke watsi da ilimin yaran talakawa da ke yankin arewacin kasar, yana mai cewa, babu yadda za a samu zaman lafiya muddin ba a bai wa yaran talakawa ilimi ba kamar yadda ake bai wa 'ya'yan attaijarai.

Talla

Yayin da yake tsokaci kan matsalolin da suka addabi yankin, Shettima wanda yanzu haka dan Majalisar Datatwa ne ya ce, babu yadda arewa za ta samun zaman lafiya da kuma ci gaba ba tare da ilmantar da 'ya'yan talakawa ba.

Tsohon gwamnan ya ce, abin takaici ne yadda shugabanni da attajirai ke daukar ‘ya'yansu suna turawa Amurka da Ingila da Dubai da Masar, yayin da suka yi watsi da ‘ya'yan talaka.

Shettima ya ce zaman lafiyar arewacin Najeriya da kuma ci gabanta ya rataya a ilmintar da ‘ya'yan talakawa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren kalaman Shettima

 

Muryar Shettima kan ilimin talakawa

 

 

Yankin arewacin Najeriya na kan gaba wajen fuskantar matsalolin tsaro a kasar, inda yake fama da hare-haren Boko Haram da na 'yan bindiga masu satar mutane don karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.