Najeriya

'Yan bindiga sun kashe 'Yan Sanda da kona ofishin su a Anambra dake Najeriya

Magoya bayan kungiyar IPOB a Najeriya
Magoya bayan kungiyar IPOB a Najeriya AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI

Rahotanni daga Jihar Anambra dake Najeriya sun ce Yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yayan kungiyar IPOB dake kokarin kafa kasar Biafra ne sun kai hari wata tashar Yan Sanda inda suka kasha jami’ai guda biyu da kuma konata baki daya.

Talla

Rahotanni sun ce Yan bindigar dauke da makamai sun kai harin ne da asubahin yau inda suka cinnawa motoci da ginin ofishin shiya na 13 wuta dake Ukpo kusa da birnin Akwa.

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Anambra da manyan hafsoshin sa sun ziyarci cibiyar, yayin da aka bayyana sunayen Yan Sandan da suka mutu a matsayin Sufeto Ishaku Aura da Uzoma Uwaebuka.

A baya bayan nan de ‘yayan wannan haramcaciyar kungiya ta IPOB sun kaddamar da munanan hare hare kan cibiyoyin Yan sanda da kuma gidan yari, inda suka saki firsinoni kusan 2,000 a Jihar Imo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.