Najeriya-shari'a

Gwamnonin Najeriya sun amince da cin-gashin kan bangaren shari'a

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu gwamnonin jihohin kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu gwamnonin jihohin kasar. Presidential Office/Handout via REUTERS

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana amincewarta da dokar cin-gashin-kai ta hukumomin shari’a da kuma majalisun dokokin jihohi, abin da ake sa ran zai kawo karshen yajin aikin da ma’aikatan Shari’a suka tsunduma makwanni biyu da suka gabata.

Talla

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya bayyana amincewar gwamnonin da cin-gashin kan hukumomin shari’ar da majalisun dokokin jihohin, inda ya ce,

Mun cimma matsaya kan maganar cin gashin hukumomin shari’a da majalisun jihohi. Wannan matsala tuni mun warware ta a tsakaninmu, kuma ba wani gwamna da bai amince ba. Kuma mun fara tsara hanyar da za mu bi wajen aiwatar da wannan kuduri. Da zarar an kammala za a fara aiki da shi nan zuwa karshen watan Mayu mai kamawa.”

 

A nata bangaren Kungiyar Ma’aikatan Kotunan ta bakin Musbahu Abubakar, jami’in huda da jama’a na kungiyar reshan babban birnin tarayya, Abuja ta ce,

In dai za a iya tunawa ko a shekarar 2014, sai da wata babbar Kotun shari’a a birnin na Abuja ta tabbatar da sashin tsarin mulkin da ke magana akan cin gashin kan hukumomin shari’ar da na majalisun jihohin, amma kungiyar gwamnonin ta ci gaba da jayayya.

Ma’aikatan Kotunan sun tsunduma cikin yajin aikin ne tun daga ranar 6 ga watan nan na Afrilu, lamarin da ya jefa ayyukan shari’a cikin halin ni-‘ya-su.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Muhammad Kabir Yusuf daga birnin Abuja

 

Gwamnonin Najeriya sun amince da cin-gashin kan bangaren shari'a

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.