Najeriya-Boko Haram

Sojin Najeriya sun kashe kwamandojin Boko Haram

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya REUTERS/Eric Gaillard

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wasu manyan kwamandojin kungiyar ISWAP a lugudan wutar da suka yi musu biyo bayan harin da mayakan suka kai sansanin sojin kasar a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Talla

Da yammacin Lahadin da ta gabata ne, mayakan cikin tarin motoci masu sulke suka far wa garin Dikwa, kafin daga bisani su tsere bayan shafe tsawon lokaci ana dauki-ba-dadi da su.

Sanarwar da rundunar sojin Najeriyar ta fitar, na cewa gomman ‘yan ta’addan sun kai harin ne a daidai lokacin da mazauna garin ke shirin bude baki na azumi.

Kakakin rundunar Brigadier General Mohammed Yerima, ya ce a gaggauce sojojin suka janye zuwa garin Gulumba Gana, daga bisani sojin sama suka yi musu lugudan wuta.

Yerima ya kara da cewa ko a ranar Litinin, sojojin sun mayar da martani tare da kwace babban shalkwatar mayakan da ke Dikwa, abin da ya kai ga lalata musu tarin makamai da kuma  kashe da dama daga cikinsu da suka hada da manyan kwamandojinsu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.