Najeriya-Ta'addanci

Mun amince a kashe daukacin 'yan bindiga- El-Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i. © Twitter@GovKaduna

Gwamnan Jihar Kaduna ta Najeriya, Nasiru El-Rufa’i ya ce, daukacin gwamnonin jihohin kasar 36 sun cimma matsayar bai-daya kan bukatar kashe duk ‘yan bindiga da sauran miyagun da ke buya a cikin dazuka.

Talla

EL-Rufa’i ya bayyana kisan daukacin ‘yan ta’addan da ‘yan bindigar a matsayin hanya daya tilo wajen tabbatar da tsaro da yankunan da ke fama da tashin hankali a sassan kasar.

A cewarsa, dole ne jami’an tsaro su kutsa cikin dazukan domin murkushe ‘yan bindigar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a birnin Abuja a wani taron tattaunawar koli kan ware kudin kula da makarantu tare da samar da tsaro a fagen neman ilimi wanda Ma’aikatar Kudi da Kasafi ta kasar ta shirya.

Shi kuwa gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Kasar, Dr. Kayode Fayemi ya bayyana matsalar zaman-kashe wando a matsayin tushen tabarbarewar tsaro a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.