Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar Greenfield a Kaduna

Wasu Jami'an tsaron Najeriiya da ke shirin shiga aikin ceto dalibai daga hannun 'yan bindiga.
Wasu Jami'an tsaron Najeriiya da ke shirin shiga aikin ceto dalibai daga hannun 'yan bindiga. AP - Ibrahim Mansur

‘Yan bindiga a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya sun farmaki wata jami’a mai zaman kanta tare da kashe malami guda baya ga sace daliban da ba a kai ga bayyana adadinsu ba.

Talla

Tun cikin watan Disamban bara al’amuran tsaro suka sake tabarbarewa a sassan arewacin Najeriya inda ‘yan bindiga ke ci gaba da farmakar  makarantu da kwalejojin Ilimi ta yadda s uke karbar kudaden fansa gabanin sakin wadanda suka kame.

Kakakin ‘yan sandan yankin da lamarin ya faru Mohammed Jalige ya ce da misalin karfe 8 da mintuna 15 na daren jiya Talata ne ‘yan bindigar suka farmaki makarantar tare da sace daliban wadanda ba a kai ga gano adadinsu ba.

A cewar kakakin ‘yan sanda har yanzu suna  ci gaba da bincike don gano alkaluman daliban da ‘yan bindigar suka sace gabanin daukar mataki naga ba.

Sai dai a cewarsa tuni aka aike da tawagar jami’an tsrao ta musamman don bin sahun ‘yan bindigar tare da ceto daliban.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya kuma tabbatar da kisan malamin jami’ar ta Greenfield guda yayin da ya sanar da shirin daukar matakan ceto daliban da ke hannun ‘yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.