'Yan sandan Ghana sun kama fursunonin Najeriya

Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Ghana
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Ghana Daniel Finnan

'Yan sandan Ghana sun sanar da kama fursunoni 9 daga cikin sama da 1,800 da suka tsere daga Najeriya lokacin da masu fafutukar kafa kasar Biafra suka fasa gidan yarin jihar Imo.

Talla

Babban jami’in 'yan sandan Ada Francis Somian ya ce, sun kama fursunonin ne sakamakon tsegunta musu da aka yi lokacin da suka shiga cikin kasar akan hanyarsu ta zuwa Birnin Accra.

Jami’in ya ce lokacin da suka kama fursunonin suna dauke da takardar shaida da kuma kudaden Najeriya da Ghana.

A ranar 5 ga watan Afrilu ne mayakan IPOB suka kai hari Cibiyar 'Yan Sanda da gidan yarin Jihar Imo inda suka kubutar da  kusan daukacin fursunonin da ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.