Najeriya-Matsalar tsaro

Ba za mu iya kawo karshen ta’addanci ba tare da makamai ba – Sojin Najeriya

Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.
Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru. © ©Daily Post Nigeria

Babban hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, ya ce dakile ayyukan ta’addanci, satar mutane da masu neman ballewa daga kasar ba zai yiwu ba idan babu makaman yakin da ake bukata.

Talla

Saboda da haka ya bukaci majalisar dokokin kasar su gaggauta duba mahimman bukatu a yayin da suke aiki a kan kasafin kudin kasar.

Ya yi wannan bayanin ne yayin wata ziyara a da kwamitin soji na majalisar dattawa, karkashin shuganasa, Sanata Ali Ndume ya kai shelkwatar soji dake Abuja.

Attahiru ya ce idan har ana so a shawo kan wannan matsala ta tsaro, dole a sama wa sojin kasar makaman da take bukata kamar su motoci masu sulke da kuma abubuwan da za su taimaka wajen yaki.

A nasa jawabin, sanata Ali Ndume ya ce rundunar sojin kasar na da gagarumin aikin warware matsalolin tsaro da suka addabi sassan kasar, inda ya kara da cewa majalisar dokoki ta taka mahimmiyar rawa wajen goyn bayan sojin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.