Najeriya

CAN ta nesanta Pantami da kisan Yakowa

Ministan sadarwar Najeriya Dr Isa Ali Fantami
Ministan sadarwar Najeriya Dr Isa Ali Fantami © Isa Ali Fantami

Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Jihar Kaduna ta bukaci Yan kasar da su nesanta ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami daga hadarin da yayi sanadiyar mutuwar tsohon Gwamnan Jihar Ibrahim Yakowa.

Talla

Yayin da yake mayar da martani kan zargin da ake yiwa ministan cewar ya jagoranci wani taron dake adawa da zaman Yakowa Gwamnan Kaduna, shugaban kungiyar John Hayab ya bukaci 'Yan Najeriya suyi watsi da wannan zargi.

Hayab wanda shine mai baiwa Yakowa shawara kan harkokin addini lokacin mulkin sa yace a matsayin sa na wanda yake kusa da marigayin bai dace a danganta rasuwar tsohon gwamnan da ministan ba, inda yake cewa yin haka zai jefa zaman lafiyar Najeriya cikin hadari.

Dole a kawo karshen wasu kasidu dake naman kawo tashin hankali

Shugaban kungiyar ya bukaci jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kawo karshen kasidun da yanzu haka a rabawa a cikin kasar wadanda ke neman tinzira tashin hankali, yayin da yace kungiyar da iyalan Yakowa basu ji dadin abinda ke faruwa ba.

Hayab yace duk wadanda ke tunanin cewar suna da wasu bayanai da zasu taimakawa jami’an tsaro gudanar da bincike kan aikata wani laifi suna da hurumin yin haka bisa yadda doka ta tanada.

Shugaban kungiyar yace a matsayin sa na shugaba ya yi Magana ne saboda hakan ya zama wajibi, amma bai dace ace saboda baka son mutuum ba sai ka goyi bayan zargin da aka masa wanda bashi da makama balle tushe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.