Najeriya

Fitaccen jarumin Nollywood ya shiga hannun Ƴan sanda saboda Fyaɗe

'Yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya Reuters

Ƴan Sanda a Jihar Lagos dake Najeriya sun kama wani fitaccen ‘dan shirin fina finan Nollywood da ake kira Olarenwaju James ko kuma Baba Ijesha saboda tuhumar da ake masa na yiwa wata karamar yarinya fyade.

Talla

Kakakin rundunar 'Yan Sandan Jihar Muyiwa Adejobi yace wata Princess Adekanya ce ta  gabatar da kara akan Baba Ijesha ne ranar Litinin a ofishin su dake Sabo abinda ya sa aka kama shi.

Jami’in yace wanda ake tuhuma ya amsa laifin sa kuma faifan bidiyon da ake sanyawa a gine gine ya dauki hotan sa lokacin da yake aikata aika aikan.

Tun tana karama ya fara lalata da yarinyar

Kakakin 'Yan Sandan yace binciken su ya nuna cewar tun yarinyar nada shekaru 7 Baba Ijesha ke lalata da ita har zuwa wannan lokaci da take da shekaru 14.

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Lagos Hakeem Odumosu ya bada umurnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin wanda tuni aka tasa keyar Baba Ijesha zuwa Sashen binciken na rundunar Yan Sandan dake Panti a Yaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.