Najeriya - Ta'addanci

Najeriya ta bayyana dalilan da ke hana ruwa gudu wajen kawo karshen ta'addanci

Wani sojan Najeriya yayin sintiri a kusa da kogin Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya
Wani sojan Najeriya yayin sintiri a kusa da kogin Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya © FLORIAN PLAUCHEUR / AFP

Gwamnatin Najeriya ta bayyana wasu dalilai da tace suke haifar da tarnaki wajen shawo kan matsalolin ayyukan ta’addancin da suka addabi kasar wadanda ke haifar da asarar dimbin rayuka da kuma dukiyoyin jama’a.

Talla

Ministan ayyuka na musamman George Akume ya bayyana matsalolin da suka hada da rashin shirin ko ta kwana da kai daukin gaggawa da kuma manufofin gwamnati akai.

Akume yace babu yadda Najeriya zata samu nasarar yaki da ayyukan Yan bindiga da kuma ta’addanci ba tare da sanya hannun yan kasa ba, saboda haka ya dace kowa ya sanya hannu wajen ganin an samu nasara akai.

Rashin kula da 'yan gudun hijara

Ministan ya yi kuma tsokaci akan matsalar da ake samu wajen kula da 'yan gudun hijirar da suka fuskanci matsaloli daga wadannan 'yan bindiga, abinda ke nuna yadda hukumomin gwamnati da aka dorawa alhakin kula da su ke karo da juna wajen sauke nauyin dake kan su saboda rahsin ingantaccen tsari.

Saboda haka ministan yace ma’aikatar sa ta sake fasalin yadda za’a aiwatar da tsare tsaren da suka kama daga kai dauki ga mutanen da suka fuskanci irin wannan iftila’in zuwa rawar da hukumomin gwamnatin da abin ya shafa zasu taka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.