Najeriya-'Yan bindiga

Wadanda suka sace daliban jami'a a Kaduna sun nemi Naira miliyan 800

Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga. Getty Images/iStockphoto - zabelin

‘Yan bindiga da suka sace wasu daliban jami’ar Greenfield dake garin Kasarami na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun tuntubi dangin daliban ta wayar salula, inda suka bukaci a biya kudin fansa na naira miliyan dari 800.

Talla

A ranar Talata da misalin karfe 8 da minti 45 ne aka sace wadannan dalibai tare da wata ma’iakaciya mai kula da wajen kwanan daliban, sanan aka kashe wani ma’aikacin jami’ar.

Rahotanni daga garin na Kasarami na cewa ba don jami’an tsaro na rundunar Operation Thunder Strike sun shiga lamarin da hanzari ba, da ‘yan bindigan sun wuce da daliban da adadinsu ya zarta wadanda suka diba.

Kakakin runduna ‘yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce rundunar na iya kokarinta wajen ceto daliban.

Daya daga cikin iyayen daliban da ya nemi a sakaya sunasa ya ce ‘yan bindigan sun nemi a biya kudin fansa har naira miliyan dari 800 don kubutar da daliban da ba a kai ga sanin adadinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.