Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane 45 a wasu kauyuka 6 dake Zamfara

Wasu daga cikin mutanen da suka cira da rayukan su daga yankin Gusau na jihar Zamfara
Wasu daga cikin mutanen da suka cira da rayukan su daga yankin Gusau na jihar Zamfara - AFP/Archivos

'Yan Bindiga a Najeriya sun kashe akalla mutane 45 lokacin da suka kai hare hare cikin wasu kauyuka 6 dake Jihar Zamfara, yayin da suka kona gidaje da shaguna da kuma gine ginen hukuma.

Talla

Rahotanni daga Jihar sun ce an kai harin ne a Yankin Magami dake karamar hukumar Gusau wanda ya shafi garuruwan Yan Doka da Kango da Ruwan Dawa da Madaba da Arzikin Da da Mairairai.

 

 

Shaidun gani da ido sun shaidawa Jaridar Daily Trust cewar Yan bindigar sun fara kai hari ne a kauyen Yan Daka dake kusa da Magami akan Babura, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Wani da ya tsira da ran sa bayan harin yace mutane da dama sun fantsama cikin daji domin tsira da rayukan su, kuma har ya zuwa yanzu babu wanda ya san ko tsira ko kuma Yan bindigar sun harbe su.

Makaman da 'Yan bindiga ke amfani da su wajen kai hari
Makaman da 'Yan bindiga ke amfani da su wajen kai hari (c) Conflict Armament Research

Rahotanni sun ce Yan Saikai sun yi kokarin kai dauki amma abin yafi karfin su saboda makaman da Yan bindigar ke dauke da su.

Jaridar tace kakakin Yan Sandan Jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya bukaci lokaci domin tabbatar mata da aukuwar lamarin, yayin da kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara ya gabatar da wata sanarwa amma wadda ke Allah wadai da harin da aka kai garuruwan Gobirawa da Gora da Rini da kuma Madoti Dankule dake karamar hukumar Maradun.

Sanarwar tace Gwamnan Jihar Bello Muhammad Matawalle yayi Allah wadai da harin, yayin da ya jajantawa mutanen da lamarin ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.