Najeriya-Chadi

Najeriya za ta girke dakaru a iyakar Chadi don kaucewa kwararar makamai

Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru.
Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru. © ©Daily Post Nigeria

Nigeria za ta tura karin Sojojinta kan iyakarta da kasar Chadi domin kaucewa kwararar kananan makamai, sakamakon yiyuwar rikicin shugabanci da ke iya faruwa a Kasar Chadi bayan rasuwar shugaba Idris Deby Itno. Daga Abuja, ga karin bayanin wakilinmu Muhammad Kabir Yusuf.

Talla

A Talatar da ta gabata ne shugaba Idriss Deby ya rasa ransa bayan samun raunuka a wata karawa da 'yan tawayen FACT masu kokarin kifar da gwamnatinsa, mutuwar da ke matsayin babbar barazana ga tsaron kasashen yankin tafkin Chadi.

Tun bayan rasuwar Deby jagora a yaki da Boko Haram, hankulan kasashen yankin na Tafkin Chadi ya tashi dangane da makomar yakin da ake da ta'addancin da ya dabaibaye yankin.

Bayan matakin nadin Mahatma Deby a matsayin jagoran Majalisar Sojin da za ta shugabanci kasar ta Chadi, wasu bayanai na nuna yiwuwar fuskantar rikicin shugabanci ga wadanda za su yi adawa na nadin sabon jagoran kuma dan tsohon shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.