Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun kashe 3 daga daliban jami'ar Greenfield da suka sace

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce 'yan bindigar da suka kutsa kai cikin Jami’ar Greenfield suka kwashe dalibai a wannan mako sun kashe guda 3 daga cikin su.

Talla

Kwamishinan tsaro Samuel Aruwan shi ne ya sanar da kisan, bayan ya tabbatar da kama dalibai da dama da ya zuwa yanzu ba a iya tantance yawan su ba.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewar ba za ta tattauna da 'yan ta’adda ko kuma biyan kudin fansa domin sakin wani mutum da aka yi garkuwa da shi ba.

Yanzu haka wasu daga cikin daliban kwalejin koyar da aikin gona na can tsare a hannun 'yan bindigar wadanda suka kwashe 39 daga cikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.