Najeriya-Kano

Mahaifiyar Sarkin Kano ta rasu

Taswirar masararutar Kano.
Taswirar masararutar Kano. © Kano Emirate council

Rahotanni daga Jihar Kano da ke Najeriya sun ce Allah ya yi wa mahaifiyar Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wato Hajiya Maryam rasuwa a wani asibiti da ke birnin Alkahira dake kasar Masar.

Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta jiyo ta bakin Awaisu Abbas Sanusi da ke aiki da Sakataren Masarautar Kano na cewa Hajiya Maryam ta yi fama da rashin lafiya kafin rasuwar ta ta.

Sanusi ya bayyana cewar nan gaba za’a sanar da lokacin da za’a yi wa Hajiya Maryam jana’iza.

Mahaifiyar Sarkin mai shekaru 86, ita ce kuma mahaifiyar Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero, kuma ta fito ne daga gidan Sarautar Ilorin dake Jihar Kwara, inda take ‘yar uwa ga Sarki Sulu Gambari da kuma Babban Hafsa a fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.