Najeriya-Katsina

'Yan sandan Katsina sun kashe dan bindiga tare da ceto wani mutum da dabbobi

Jami'an 'yansandan Najeriya.
Jami'an 'yansandan Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

‘Yan sanda sun yi nasarar kashe wani dan bindiga, kana suka ceto wani wanda aka sace bayan wata musayar wuta da ‘yan bindigar da suka kutsa kauyen Kwanar Kodo dake karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina a Najeriya.

Talla

‘Yan sandan sun kuma kwato shanu 20 da rahuna 100 a wani samame da suka kai kusan karshen mako.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen Kwanar Kodon ne da misalin karfe 2:30 na daren  Juma’a sukaa kuma dauki wani mutum mai suna Alhaji Sanusi Adamu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Gambi Isa ya tabbatar da aukuwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.