Najeriya - IPOB

Jami'an tsaro sun kashe babban kwamandan kungiyar IPOB a Imo

Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya.
Wani jami'in dan sanda a birnin Legas dake tarayyar Najeriya. AP - Sunday Alamba

Jami’an tsaro sun bindige kwamandan haramtacciyar kungiyar IPOB, mai neman ballewa daga Najeriya wanda ya jagoranci harin da aka kai Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Imo.

Talla

Rahotanni suka ce a safiyar jiya Asabar, jami’an tsaron hadin gwiwar sojoji da ’yan sanda da DSS suka hallaka ‘Ikonso Commander’ tare da shida daga mambobinsa kana aka cafke wasu a maboyarsu da ke kauyen Oromama da ke Karamar Hukumar Oru ta Gabas a Jihar.

Jami’an tsaron sun kuma kwato tarin makamai a samamen da suka kai bayan da ’yan bindigar suka kai hari a gidan Gwamnan Jihar, Hope Uzodinma, suka kashe jami’an tsaro.

 Farmakin gidan gwamnan jihar

Wani babban jami’i a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Kasa ya ce a yayin bin sawun maharan ne jami’an tsaron suka kai samamen a maboyar IPOB da ke kauyen.

“Jami’an tsaron na tunkarar wurin sai ’yan kungiyar suka bude musu wuta babu kakkautawa; Su kuma nan take suka mayar da martani.

“Sun kashe babban kwamandan ’yan tawayen na yankin Kudu maso Gabas wanda ake wa lakabi da ‘Ikonso Commander’ da wasu mayakan kungiyar guda shida.

Jami'in yace, “Ikonso shi ne mataimaki kuma mai shirya hare-haren da kungiyar take kaiwa a wurare daban-daban.

“Shi ne ya kitsa ya kuma jagoranci harin da aka kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar Imo da wasu hare-haren da aka kai wa jami’an tsaro da sansanoninsu,” inji majiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.