Najeriya-Hare-hare

An kashe kusan mutane 240 a mako guda a Najeriya

Jami'an tsaron Najeriiya na cikin wadanda aka hallaka
Jami'an tsaron Najeriiya na cikin wadanda aka hallaka AP - Ibrahim Mansur

A cikin mako guda, an kasha mutane akalla 239 a Najeriya da suka hada da jami’an tsaro, sannan aka yi garkuwa da 44, lamarin da ke dada fito da matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.

Talla

An yi kisan ne a sassan kasar da suka hada da babban birnin tarayya Abuja da ke zama fadar gwamnatin kasar.

Alkaluman da aka tattara sun nuna cewa, an kashe mutane 20 a ranar Lahadi ta makon sama, 5 a ranar Litinin, sai 6 a ranar Talata, inda aka kashe 85 a ranar Laraba a Karamar Hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Kazalika an salwantar da rayukan mutane 60 a kauyen Magami a ranar Juma’ar da ta gabata.

Haka ma wasu dalibai 3 na Jami’ar Greenfiled mai zaman kanta a jihar Kaduna sun rasa rayukansu bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su, yayin da wasu jami’an ‘yan sanda a jihar Anambra su ma suka mutu a wani farmaki da aka kaddamar kan shalkwatansu.

Hare-hare a sassan Najeriya sun tsananta, inda ‘yan bindiga ke far wa kauyuka da kasuwanni da wuraren ibada har ma da matafiya da ke bin babbar hanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.