Najeriya-Boko Haram

Jirgin Sojin Najeriya ya yi kuskuren luguden wuta kan Sojin kasa

Jirgin Sojin saman Najeriya.
Jirgin Sojin saman Najeriya. naij.com

Rahotanni daga Najeriya sun ce akasarin sojin da suka mutu sakamakon harin boko haram a Mainok da ke Jihar Borno sun mutu ne sakamakon harin sama da jirgin yakin Najeriya ya kai musu cikin kuskure.

Talla

Bayanan da ke zuwa na nuna cewa yayinda wasu daga cikin sojojin suka rasu sakamakon artabu da mayakan boko haram akasarin su sun mutu ne sakamakon harin da jirgin sojin ya kai musu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana cewar ana yada faifan bidiyon yanzu haka a kafofin sada zumunta.

Kakakin rundunar sojin saman Najeriya Edward Gabwet ya shaidawa Jaridar cewar shi ma ya ga bidiyon amma ba zai iya tabbatar da afkuwar lamarin ba.

Jami’in ya ce za su gudanar da bincike idan sun tabbatar da sahihancin bidiyon za su kaddamar da bincike kan lamarin.

Wannan shi ne kazamin hari na baya bayan nan da ya ritsa da sojojin Najeriya wadanda ke yaki da boko haram a arewa maso gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.