Najeriya-Boko Haram

Rahoto kan kisan Sojojin Najeriya 32 a farmakin Boko Haram

Wasu sojojin Najeriya da ke yakar kungiyar Boko Haram.
Wasu sojojin Najeriya da ke yakar kungiyar Boko Haram. AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE

Akalla Sojojin Najeriya 32 suka rasa rayukan su sakamakon kazamin harin da mayakan boko haram suka kai kan tawagar sojojin da ke dauke da makamai zuwa Birnin Maiduguri.Mayakan na kungiyar ISWAP sun yi amfani da makaman roka da ke dauke da gurneti wajen kai harin, kamar yadda za kuji Karin bayani daga wakilinmu na Maiduguri, Bilyaminu Yusuf.