Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban jami'ar ayyukan Noma a Benue

Sace daliban na zuwa dai dai lokacin da 'yan bindigar ke ci gaba da garkuwa da daliban jami'ar Greenfield a Kaduna.
Sace daliban na zuwa dai dai lokacin da 'yan bindigar ke ci gaba da garkuwa da daliban jami'ar Greenfield a Kaduna. © PHOTO/FOTOSEARCH

Hukumomin Jami’ar kula da ayyukan noma da ke Jihar Benue a Najeriya sun sanar da cewar wasu 'yan bindiga sun kutsa kai cikin ta jiya da yamma inda suka kwashe daliban da ba’a san yawan su ba suka gudu da su.

Talla

Daraktar yada labaran Jami’ar Rosemary Waku ta sanar da lamarin wanda ta ce ya faru ne jiya lahadi a harabar makarantar da ke birnin Makurdi.

Jami’ar ta ce tuni suka sanar da hukumomin tsaro abinda ya faru, kuma ya zuwa yanzu basu ji duriyar daliban ba ko kuma wadanda suka yi garkuwa da su.

Wannan lamari na zuwa ne kasa da mako guda bayan sace daliban Jami’ar Greenfield da ke Kaduna wadanda aka kashe 3 daga cikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.