Buhari na neman taimakon duniya kan matsalar tsaro
Wallafawa ranar:
Shugaba Muhammadu Buhari ya roki kasashen duniya da zu taimaka wa Najeriya da kasashen kudu da sahara wajen magance matsalar tsaro domin hana yaduwarta.
Shugaban na Najeriya ya nemi agajin ne a wani taron kafar bidiyo da Sakatarten Harkokin Wajen Amurka, Mr. Anthony Blinken.
Buhari ya bukaci Amurka da ta yi nazari kan maido da rundunar AFRICOM daga Jamus zuwa nahiyar Afrika domin karfafa matakan magance matsalar tsaro a nahiyar.
Kalubalen tsaro a Najeriya na ci gaba da zama abin damuwa a gare mu wanda kuma ke mana mummunan tasiri ganin halin matsiln lambar da ake fuskanta a Sahel da Tsakiyar Afrika da kuma Yammacin Afrika har ma da yankin Tafkin Chadi” inji Buhari.
Shugaban ya kara da cewa, Najeriya za ta inganta hadin-guiwarta da aminanta domin aiki tare wajen samar da tsaro ga kowa.
Najeriya na cikin kasashen Afrika da ke fama da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram baya ga matsalar 'yan bindiga da ke kisa babu kakkautawa tare da sace jama'a domin karbar kudin fansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu