Najeriya-Tsaro

Rahoto kan shirin kungiyoyin arewa na kafa rundunar tsaro

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya.
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya. AFP PHOTO /STRINGER

Ganin yadda matsalolin tsaro suka addabi yankin Arewacin Najeriya da suka hada da Boko Haram da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane da kuma rikici tsakanin makiyaya da manoma, gamayyar kungiyoyin ‘yan arewacin kasar ta bayyana shirin kafa rundunar tsaro domin ganin an ceto yankin sakamakon gazawar gwamnati.Muhammad Sani Abubakar na dauke da rahoto daga Abuja.