Najeriya-Rashawa

Rashawa za ta hana Najeriya ci gaba - Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Kano State Government

Gwamnan jihar Kano a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce kasar ba za ta samu ci gaba ba saboda cin hanci da rashawar da ya dabaibaye ta.

Talla

Ganduje ya bayyana hakan ne jiya Alhamis yayin kaddamar da wani kwamiti mai mutune takwas kan wasu dabarun yaki da rashawa a jihar.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji ya wakilce shi, ya kaddamar da kwamitin ne a da nufin rage cin hanci da kuma tabbatar da gudanar da al'amura  a bayyane a fadin jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.