Najeriya-Zamfara-Katsina

Tubabben dan bindiga da ya kitsa satar daliban Kankara ya koma daji

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos

Rahotanni daga Najeriya sun ce mutumin da ya jagoranci sace daliban makarantar Sakandaren Kankara dake Jihar Katsina daga bisani kuma ya bayyana aje makaman sa, Auwal Daudawa ya sake daukar makamai inda ya shiga daji.

Talla

Bayanai sun ce Daudawa da ya mika bindigogi 20 a bikin da Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya, yanzu haka yana wani daji dake kusa da iyakar Zamfara da Katsina.

Dan bindiga, Auwalun Daudawa ne ya kitsa sace daliban makarantar sakandaren Kankara ta jihar Katsina a ranar 12 ga watan Disamban shekarar 2020, satar dalibai irinta ta farko da wata kungiya ta taba yi bayan Boko Haram.

Majiyoyi kusa da Daudawan sun ce ya kwashe iyalansa da mukarrabansa zuwa gandun dajin Jaja a karamar hukumar Zurmi ita jihar Zamfara a ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.