Najeriya-'Yan bindiga

Daudawa da ya jagoranci sace daliban Kankara ya mutu a hannun 'Yan bindiga

Daya daga cikin daliban sakandaren Kankara na jihar Katsina lokacin ganawa da shugaban kasa bayan sakin da yan bindiga suka yi
Daya daga cikin daliban sakandaren Kankara na jihar Katsina lokacin ganawa da shugaban kasa bayan sakin da yan bindiga suka yi Kola SULAIMON AFP/File

Rahotanni daga Najeriya na cewa an kashe Auwalun Daudawa, dan bindigar nan da ya jagoranci garkuwa da daliban sakandaren Kankara da ke jihar Katsina wanda tuba sannan ya sake komawa ruwa a wannan makon.

Talla

Kwanaki huɗu bayan da ya janye tubar da ya yi  tun farko ya kuma koma daji, Auwal Daudawa, wanda aka fi sani da rawar da ya taka wajen sace daliban sakandaren Kankara sama da 300 a jihar Katsina ya gamu da ajalinsa ne sakamakon wani rikicin hamayya a dajin.

Wasu majiyoyi da amintattu sun sanar da jaridar Daily Trust a Najeriya cewa an kashe Daudawa ne da yammacin ranar Juma’a a lokacin da suke musayar wuta da wasu gungun abokan hamayyarsu a dajin Dumburum da ke tsakanin karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara da karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Ya sake shahara bayan tuba

Shahararren dan fashin ya yi kaurin suna bayan da ya kitsa kai hari a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kankara inda ya sace sama da ’yan makaranta 300 a cikin dare.

Watanni biyu bayan haka, dan fashin ya bayyana a Gusau, babban birnin Zamfara, tare da mutanensa biyar inda ya sanar da tubarsa tare da mika bindigogin AK 20 da wasu makamai ga ‘yan sanda.

A ranar Alhamis, rahotonni suka tabbatar da komawarsa ruwa, inda ya bar sabon gidansa a Damba, dake wajen garin Gusau don komawa daji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.